Super Eagles ba ta gayyaci Mikel da Moses ba

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Nigeria da Afirka ta Kudu sun kara a 2015 inda suka tashi wasa 2-2

Genort Rohr bai gayyaci Mikel Obi da Victor Moses zuwa tawagar kwallon kafa ta Super Eagles ba.

Tawagar ta Nigeria za ta buga wasan shiga gasar cin kofin Afirka da za a yi a 2019, wanda Kamaru za ta karbi bakunci.

Super Eagles ba ta gayyaci Moses ba duk da yana kan ganiyarsa a tamaula, yayin da Mikel ke fama da jinya.

Haka suma Brown Ideye da Odion Ighalo ba za su buga wa Nigeria karan battar ba.

Rohr ya sanar da 'yan wasa 23 da za su kece raini da Afirka ta Kudu a ranar 10 ga watan Yuni a filin wasa na Akpabio da ke Uyo.

Ga jerin 'yan wasan da Super Eagles ta gayyata:

Masu tsaron raga: Daniel Akpeyi, Ikechukwu Ezenwa da Dele Alampasu.

Masu tsaron baya: Elderson Echiejile, Kenneth Omeruo, Tyrone Ebuehi, Chidozie Awaziem, Shehu Abdullahi, William Ekong da Maroof Youssef.

Masu wasan tsakiya: Ogenyi Onazi, John Ogu, Oghenekaro Etebo, Alhassan Ibrahim, Mikel Agu da Wilfred Ndidi.

Masu cin kwallaye: Ahmed Musa, Kelechi Iheanacho, Alex Iwobi, Moses Simon, Henry Onyekuru, Olanrewaju Kayode da Victor Osimhen.

Labarai masu alaka