'Man City za ta dauki kofi hudu a badi'

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A bara Manchester City ta lashe League Cup karkashin Manuel Pellegrini

Shugaban Manchester City, Khaldoon Al Mubarak ya ce burin kungiyar ne ta lashe kofi hudu a badi.

Mubarak ya ce idan har City ta yi hakan, zai zama babban ci gaban da kungiyar za ta samu a tarihin tamaula.

A kakar farko da Pep Guardiola ya ja ragamar kungiyar, ta kare a mataki na uku a gasar Premier, da kaiwa wasan daf da karshe a kofin FA da matakin kungiyoyi 16 a Gasar Zakarun Turai a bana.

Mubarak ya ce 'Pep na fatan lashe kofin da yake gabansa, kuma dalilin da ya sa nake kaunarsa, nima hakan nake bukata'.

Kungiyar Manchester United ce ta lashe kofi hudu a kaka daya, inda ta ci Community Shield da League Cup da Premier League da kofin Zakarun nahiyoyin duniya da ta yi a 2008-09.

Manchester City za ta fafata a badi a gasar Premier League da FA da EFL Cup da kofin Zakarun Turai.

Labarai masu alaka