Man City ta dauki golan Benfica

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Moraes ya yi wa Benfica wasa 37 tun lokacin da ya fara buga mata tamaula a Maris din bara

Manchester City ta amince da kulla yarjejeniyar daukar mai tsaron ragar Benfica, Ederson Moraes kan kudi fam miliyan 35.

A watan Maris din bara ne Moraes mai shekara 23 ya fara buga wa Benfica tamaula, ya zuwa yanzu ya yi mata wasa 37.

Tun a ranar Lahadi a lokacin da Benfica ta doke Vitoria Guimaraes 2-1, Moraes ya ce wasansa na karshe ke nan a kungiyar.

Matashin dan kwallon tawagar Brazil wanda har yanzu bai buga mata tamaula ba, yana daga cikin wadanda aka gayyata wasan sada zumunta da za ta yi da Argentina da Australia a nan gaba.

Kocin City, Pep Guardiola ya dade yana son daukar Moraes a baya can, dalilin da ya sa ya bar Willy Caballero ya bar Ettihad domin dan kwallon ya samu gurbin zama a kungiyar.