An jaddada hana Atletico sayen 'yan wasa

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A shekarar 2015 hukumar kwallon kafa ta duniya ta samu Real Madrid da Atletico da laifi

Atletico Madrid ba za ta sayi yan wasa ba a bana, bayan da kotun daukaka karar wasanni ta tabbatar mata da hukuncin da aka yanke tun farko.

Hukumar kwallon kafa ta duniya ce ta dakatar da ita shekara biyu daga daukar 'yan wasa zuwa kaka biyu, bayan da aka same ta da laifin karya ka'idar hukumar a Yunin 2016.

A watan Disamba ne kotun ta rage hukuncin da aka yi wa Real Madrid zuwa shekara daya, wadda aka dakatar tare da Atletico.

Atletico Madrid ta ce 'hukuncin babu adalci ya kuma kawo nakasu ga kungiyar.

Sai dai kuma kotun ta rage kudin tarar da aka ci kungiyar daga fam 719,793 zuwa 439,873.

Labarai masu alaka