Zakarun Turai: Juventus da Madrid za su kece raini

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Real Madrid ta ci kofin Zakarun Turai 11, Juventus kuwa guda biyu ne da ita

A ranar Asabar za a buga wasan karshe na cin Kofin Zakarun Turai tsakanin Real Madrid da Juventus a Cardiff.

Kungiyoyin biyu sun fafata sau 18 a gasar cin kofin zakarun Turan, kuma kowacce ta ci karawa takwas da canjaras biyu.

A baya-bayan nan Juventus ta ci Madrid 2-1 a ranar 5 ga watan Mayun 2015, sannan suka tashi kunnen doki a gidan Madrid a ranar 13 ga watan a gasar ta Zakarun Turai.

Juventus ta ci Kofin Zakarun Turai guda biyu, yayin da Real Madrid ta dauki kofin sau 11.

Labarai masu alaka