Sau biyar Ronaldo ya ci Juventus

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sau 11 Real Madrid ta ci kofin Zakarun Turai

Juventus da Real Madrid za su kara a wasan karshe a Gasar cin Kofin Zakarun Turai a ranar Asabar a Cardiff.

A haduwa 18 da kungiyoyin biyu suka yi a Gasar cin Kofin Zakarun Turai, Cristiano Ronaldo ya buga hudu daga ciki.

A wasanni hudun da Ronaldo ya buga ya ci Juventus kwallo biyar.

Ronaldo ya fara cin Juventus kwallaye biyu a ranar 23 ga watan Oktoban 2013 a gasar cin kofin Zakarun Turai wasannin cikin rukuni.

A ranar 5 ga watan Nuwamba ya ci daya a karawar da suka tashi 2-2 a Italiya.

A karawar da Juventus ta doke Madrid 2-1 a ranar 5 ga watan Maris din 2015 shi ne ya ci gudan, sannan ya kara kwallo a raga a karawar da suka tashi 1-1 a Madrid a ranar 12 ga watan.

Labarai masu alaka