Yaya Toure ya tsawaita zamansa a City

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Toure ya koma City daga Barcelona a 2010

Yaya Toure ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da buga wa Manchester City tamaula zuwa shekara daya.

Toure wanda ya koma Ettihad da taka-leda daga Barcelona a 2010, ya ci kofi shida a kungiyar.

A karshen kakar bana ne yarjejeniyarsa za ta kare da City, amma ya tsawaitata zuwa shekara daya, hakan na nufin zai yi kaka takwas a Ettihad kenan.

Daraktan kungiyar Txiki Begiristain ya ce 'Yaya ya bayar da gudun mawa a City, yana kuma daga cikin 'yan wasan da suke taka rawa a kungiyar'

Labarai masu alaka