Liverpool na dab da daukar dan wasan Roma

Mohamed Salah Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Salah ya ci wa Roma kwallaye 15 a wasa 31 a kakar wasa ta bana

Liverpool na tattaunawa da Roma domin sayen dan wasan gaba na kasar Masar Mohamed Salah, bayan da Roman ta ki sallamar da dan wasan a kan kudi fam miliyan 28.

Tun da farko dai, Roma ta ki amincewa da tayin da Liverpool din tayi domin sayen dan wasan mai shekaru 24 da haihuwa, amma har yanzu Salah ne babban burin Jurgen Klopp.

An dai fahimci cewa kungiyar ta kasar Italiya na neman fam miliyan 35 zuwa fam miliyan 40 kafin ta saki Salah.

Dan wasan yana dab da zuwa Liverpool kafin komawarsa Chelsea daga FC basel a kan kudi fam miliyan 11 a watan Janairun 2014.

Salah ya taimakawa Roma sosai a gasar Serie A na bana, inda ta tashi a mataki na biyu, kuma ya ci kwallaye 15 a wasanni 31 da ya buga wa kungiyar.

Klopp ya yi amanna cewa zuwan dan wasan alheri ne ga kungiyar, wacce ke shirin komawa gasar Zakarun Turai a kakar wasa a badi.

Kungiyar ta Liverpool ta kammala shirin daukar dan wasan gaba na Chelsea, Dominic Solanke, mai shekaru 19 da haihuwa, wanda zai zo kungiyar ranar 1 ga watan Yuli.

Labarai masu alaka