Sampaoli: Messi zai cigaba da taka leda

Leonel Messi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Messi bai taba daukar kofin duniya ba

Sabon kocin Argentina Jorge Sampaoli ya ce samun nasara tare da Messi da kuma samun gurbi a gasar kofin duniya ta shekarar 2018 sune manyan kalubalen dake gabansa.

Sampaoli, mai shekaru 57 da haihuwa, ya karbi jagoranci kungiyar kwallon kafa ta kasarsa bayan barin kungiyar Sevilla bayan kakar wasa daya kawai.

Idan ba a manta ba, dan wasan Barcelonan Lionel Messi mai shekaru 29 da haihuwa, ya bayyana ritayarsa daga bugawa kasarsa kwallo a watan Yunin 2016 - amma ya sake shawara bayan watanni biyu.

Sampaoli ya ce " Na yi magana da Messi kuma muna cike da farin ciki".

Messi ya ci wa kasarsa kwallaye 58 a wasanni 117 da ya buga mata, amma kasar Argentina wacce ta dauki kofin duniya a 1978 da 1986 yanzu tana fuskantar barazanar ficewa a gasar kofin duniya a shekara mai zuwa, bayan da suka samu nasara a wasanni 6 kawai cikin wasanni 14 da suka buga.

Wasanni hudu na neman cancanta suka rage wa kasar - sune na farko da Uruguay, sai kuma da Venezuela, sai karawarsu da Peru kafin su hadu da kasar Ecuador.

Argentina ta kori kocinta Edgardo Bauza a watan Afrilu bayan da ya jagoranci kasar a wasanni takwas.

Labarai masu alaka