Kocin Arsenal Arsene Wenger yana zawarcin Riyad Mahrez

Mahrez ya zura kwallaye 10 a kakar Firimiyar ban Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mahrez ya zura kwallaye 10 a kakar Firimiyar bana

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce yana zawarcin ɗan wasan gaban Leicester City Riyad Mahrez, sai dai ba a fara maganar hakan ba a hukumance.

Ɗan wasan mai shekara 26 ya sanya hannu a kan sabon kwantiragi da kulob din Leicester City a watan Agustan bara, amma daga bisani an bukaci ya ƙara gaba.

Mahrez ya taka muhimmiyrar rawa yayin da Leicester City ta lashe Kofin Firimiyar kakar bara, amma a kakar bana sun kammala gasar ne a mataki na 12.

Yayin da aka tambayi Wenger ko sun fara zawarcinsa a hukumance? Sai ya ce "a'a, tukuna. Za mu iya nemansa kuma za mu iya ƙin nemansa," in ji shi.

Mahrez ya koma Leicester City ne daga kulob din Le Havre na kasar Faransa a shekarar 2014 a kan fam dubu 400 kuma a shekarar 2016 ya lashe kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafar gasar Ingila.

"Mahrez ya taka muhimmiyar rawa a Leicester lokacin da suka lashe Gasar Firimiya, kamar kowane dan wasan kulob din," in ji Wenger.

Ya ci gaba da cewa "Kakar bana ta sha bamban da ta bara, amma hakan ba yana nuna wata gazawa ba ne daga ɓangaren dan wasan."