Hazard ya yi rauni yayin atisaye

Eden Hazard

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Hazard ya ci ƙwallaye 16 a Gasar Firimiyar bana

Ɗan wasan tsakiyar kulob ɗin Chelsea Eden Hazard ya ji rauni a idon sawunsa na dama yayin da yake atisaye da tawagar wasan kasarsa wato Belgium , kamar yadda hukumar kwallon kafar kasar ta bayyana.

Hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter cewa dan wasan ya samu gocewar kashi a idon sawunsa kuma hoton kafar da aka dauka yana nuni da cewa tsagewar kashi ne.

Ɗan wasan mai shekara 26 ba zai buga wasan sada zumuntar da Belgium za ta yi da kasar Jamhuriyar Czech ba ranar Litinin, da kuma wasan neman gurbin Kofin Duniya da za su buga da Estonia a ranar 9 ga watan Yuni.

Sai dai ba a san tsawon lokacin da dan wasan zai kwashe ba yana jinya.

Hazard ya taka muhimmiyar rawa a nasarar da Chelsea ta samu a Gasar Firimiyar bana, inda ya zura kwallaye 16 a wasanni 36.

Yana da sauran shekara uku a Chelsea, amma an fara maganar cewa Real Madrid tana zawarcinsa.