U 21: Ingila ta ajiye Ruben Loftus-Cheek na Chelsea

Ruben Loftus-Cheek (a dama)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ruben Loftus-Cheek (na dama) ya yi wa Chelsea wasa 11 a kakar da ta kare

An fitar da dan wasan tsakiya na Chelsea Ruben Loftus-Cheek daga tawagar 'yan wasan Ingila ta 'yan kasa da shekara 21 da za ta gasar cin kofin kasashen Turai a Poland.

Dan wasan mai shekara 21 yana fama da ciwon baya ne, saboda haka kociyan tawagar Aidy Boothroyd bai sa shi a cikin jerin tawagar farko ta 'yan wasa 28 da aka rage zuwa 23 ba.

Haka shi ma dan wasan Chelsea Izzy Brown da Patrick Roberts na Manchester City ba su samu shiga tawagar ba saboda rauni.

Sunan mai tsaron raga Joe Wildsmith na Sheffield Wednesday da na dan baya Sam McQueen na Southampton ba sa cikin tawagar su ma, amma suna zaman ko-ta-kwana.

A ranar Juma'a 16 ga watan Yuni za a fara gasar a lokacin da Ingila za ta fafata fa Sweden a wasansu na farko na rukuni, wanda ya kunshi Poland da Slovakia.