Ina nan daram a Real Madrid - Gareth Bale

Gareth Bale da Kofin Zakarun Turai Hakkin mallakar hoto Others
Image caption Gareth Bale ya kafa tarihin zama dan wasan da ya dauki kofin Zakarun Turai uku daga Wales

Gareth Bale ya ce yana jin dadin zamansa a Real Madrid kuma zai ci gaba da zama tare da Zakarun Turan, domin burinsa shi ne daukar kofi, kuma yana samun hakan.

Bayan minti 77 aka sako dan wasan na Wales a ranar Asabar lokacin da Real Madrid ta doke Juventus 4-1 a Cardiff, babban birnin yankin na Wales, a wasan da Zakarun suka dauki kofin Turan na uku a cikin shekara hudu.

Ana rade-radin dan wasan mai shekara 27, wanda ya kulla kwantiragin zama a Madrid din har zuwa watan Oktoba na 2022, zai bar Bernabeu.

To amma Bale ya ce, shi kam yadda suke daukar kofi yana jin dadin zamansa, kuma daman da shi ya rattaba hannu a yarjejeniya mai tsawo ta zama a kungiyar.

Ya ce iyalinsa suna jin dadi kuma shi ma yana jin dadi, saboda haka za su ci gaba da abin da suke yi na zama a Madrid.

Tsohon dan wasan na Tottenham ya koma Real ne a 2013 a lokacin a kan kudin da shi ne ya fi duk wani dan wasa tsada na fan miliyan 85.

Bale yanzu ya shiga rukunin 'yan wasan da suka dauki Kofin Zakarun Turai uku, inda ya zama daya da Franz Beckenbauer na Jamus Johan Cruyff dan Holland.

Duk da cewa dan wasan yana fama da ciwon idon kafa, amma ya kudiri ganin ya yi wasan na karshe a babban birnin yankin nasa.

A watan Nuwamba aka yi masa tiyata, kuma ya ce idan ba domin wasan na Cardiff ba da kila ya je a sake yi masa tiyatar ciwon a karo na biyu.

Tsohon shugaban kungiyar ta Real Madrid Ramon Calderon ya ce ba shi da wani shakku Gareth Bale zai ci gaba da zama a kungiyar.

Game da rade-radin da ake yi cewa Zakarun na Turai suna sha'awar mai tsaron ragar Manchester United David de Gea, Calderon ya tabbatar da hakan.

Amma ya kara da cewa ga alama Mourinho shi ma yana sha'awar Morata, kuma kila ya yarda ya saki de Gea idan za a ba shi Moratan.