Tsohon dan wasan Newcastle Cheick Tiote ya rasu

Cheick Tiote Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dan wasan Ivory Coast Cheick Tiote ya yi wa Newcastle wasa 156

Tsohon dan wasan Newcastle na tsakiya Cheick Tiote ya rasu yana da shekara 30 bayan ya fadi a lokacin da yake atisaye da kungiyarsa ta China Beijing Enterprises.

Mai magana da yawun dan wasan Emanuele Palladino ne ya tabbatar da mutuwar tasa a ranar Litinin din nan.

Cheick Tiote ya yi wa kasarsa Ivory Coast wasa inda suka dauki kofin kasashen Afirka na shekara ta 2015.

A kwanan nan ya koma China da wasa bayan ya dade a gasar Premier tare da Newcastle United.

Dan wasan na Ivory Cosat ya yi wa Newcastle wasan Premier 139 tun bayan da ya koma can a watan Agusta na 2010 daga FC Twente toa Holland.

Wasa uku kawai dan wasan mai shekara 30 ya yi wa Newcastle din a bana, kafin ya koma kungiyar ta China a kan kudin da ba a bayyana ba.