Tennis: Andy Murray ya kai wasan dab da na kusa da karshe a Faransa

Andy Murray a gasar Faransa Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sau hudu a jere kenan Andy Murray ya kai wasan dab da na kusa da karshe a Paris

Zakaran wasan tennis na daya a duniya dan Birtaniya Andy Murray ya doke abokin karawarsa Karen Khachanov na Rasha, ya kai wasan dab da na kusa da karshe a karo na bakwai a gasar Faransa.

Cikin sa'a biyu da minti hudu gwarzon na duniya ya yi wannan nasara tasa ta 650, da ci 6-3 6-4 6-4.

Yanzu dai Murray dan yankin Scotland, mai shekara 30 zai fafata a wasan na dab da na kusa da karshe, da dan Japan Kei Nishikori, wanda shi ne na takwas a jerin gwanayen tennis.

Bayan nasarar da ya samu a wasan na French Open Murray ya jajanta wa wadanda harin Manchester da Landan ya rutsa da su.