Zakarun Turai: Sai Kungiyoyin Premier sun tashi tsaye - Alan Shearer

'Yan Real Madrid na murnar daukar kofin Zakarun Turai na 12 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Real Madrid ta dauki kofinta na Zakarun Turai na uku a shekara hudu bayan ta casa Juventus da ci 4-1

Tsohon dan wasan Ingila kuma mai sharhi a kan kwallon kafa a yanzu Alan Shearer ya ce yana sa ran kungiyoyin Premier su yi kokari a gasar Zakarun Turai ta gaba, amma sai sun tashi tsaye sosai daga yadda yaga wasan karshe na ranar Asabar na gasar.

Ya ce babu ko da daya daga cikin kungiyoyi biyar din Premier da za su shiga gasar da take ko kusa da matsayin Real Madrid ko Juventus.

Shearer ya ce sai an dage an yi aiki tukuru, kuma dole ne sai kowace kungiya daga cikinsu ta tashi tsaye ta sayi 'yan wasa kafin ta samu damar cin kofin.

Tsohon dan wasan ya ce saurin tunanin Real da yadda suke bayar da kwallo da kyau, su suka sa suka yi galaba a wasan na Cardiff, bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, inda suka taka-leda yadda ya kamata a ce kungiyoyinmu sun yi koyi da hakan.

Ya ce zakarun na Spaniya sun yi wa Juventus shigar sauri da kuma dabara, yadda suka rika taba kwallon, wanda hakan darasi ne ga kowa kan abin da ya kamata ka yi ka samu nasara a irin wannan mataki.

Ya kara da cewa bai san abin da ya faru da Juventus ba, bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, amma sun yi wasa da kyau kafin a tafi hutu, kuma duk tsawon kakar wasan nan suna da baya mai kyau.

Alan Shearer ya ce tun kafin wasan na karshe na Zakarun Turan, ya san cewa kungiyoyin Premier suna da jan aiki a gabansu kafin su kamo Real Madrid da Juventus.

Kuma kallon wasan karshen ya tabbatar masa cewa ratar ma ta fi yadda ya yi hasashe, amma kuma yana da yakinin cewa lamarin zai sauya.