Pepe zai bar Real Madrid

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shekara 10 Pepe ya yi yana taka-leda a Real Madrid

Mai tsaron bayan Real Madrid, Pepe zai bar kungiyar bayan shekara goma yana taka-mata leda.

Pepe mai shekara 34 wanda aka haifa a Brazil amma yake buga wa tawagar kwallon kafa ta Portugal kwallo ana alakanta shi da zai koma Paris St Germain ko kuma AC Milan da wasa.

Dan kwallon ya yi wa Real wasa 334, ya kuma lashe kofin La Liga uku da na Zakarun Turai shi ma guda ukun.

Pepe bai buga karawar da Madrid ta doke Juventus 4-1 ba, sai dai ya ce bai yi ban kwana da kungiyar ba, amma ta san zai bar ta.

A wata hira da aka yi da shi a gidan radiyon COPE ya ce 'bai yi magana da Zinedine Zidane tun bayan da kungiyar ta ci kofin Zakarun Turai na 12 jumulla ba'.

Pepe ya kara da cewa 'Zidane ya yi bajinta a Madrid, amma akwai wasu abubuwa da suke gudana wanda bai amince da su ba'.