Arsenal ta dauki mai tsaron baya Kolasinac

Hakkin mallakar hoto Arsenal
Image caption Kolasinac zai saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyar a Arsenal

Arsenal ta sanar da daukar mai tsaron bayan Schalke 04, Sead Kolasinac.

Dan kwallon tawagar Bosnia-Herzegovina zai koma Arsenal a ranar 1 ga watan Yuli, a matsayin wanda ba shi da yarjejeniya da wata kungiyar.

Kuma kafin a kammala cike takardun ka'ida, dan wasan mai shekara 23, zai iya fara yin atisaye a Arsenal tare da 'yan wasan kungiyar.

Kolasinac ya taimaka wa Schalke ta kare a mataki na 10 a teburin Bundesliga, kuma kungiyar ta kai wasan daf da na kuda da karshe a Europa League.

Labarai masu alaka