Real Madrid ce ta fi yin fice a Turai

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A ranar Asabar Real Madrid ta doke Juventus da ci 4-1 ta lashe Kofin Zakarun Turai na 12 jumulla

Real Madrid ce kungiyar da ta fi yin fice a Turai, bayan da ta dauki Kofin Zakarun Turai a karo na uku a shekara hudu wanda shi ne kofin da ta dauka na 12.

A cewar kididdigar kamfanin Gracenote, wanda ke auna kokarin kungiyoyin Turai, Chelsea da Manchester City ne kungiyoyin Ingilka da ke goman farko.

Chelsea tana mataki na bakwai, ta kuma dara Manchester City, wadda ke mataki na takwas, duk da ba ta buga gasar cin Kofin Zakarun Turai na bana ba.

Real Madrid, wadda ta dauki kofin La Liga, ta maye gurbin Barcelona wadda ita ce ke kan gaba a da.

Arsenal ce ta 11, abokiyar hamayyarta Tottenham kuma tana mataki na 13, Manchester United kuwa tana ta 16.

Ana auna kokarin kungiyoyin Turan da sakamakon wasannin shekara hudu da suka wuce.

Labarai masu alaka