Southampton za ta yi karar Liverpool kan Van Dijk

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Van Dijk ya koma Southampton daga Celtic a Satumbar 2015

Southampton za ta yi karar Liverpool ga mahukuntan Premier, kan tuntubar mai tsaron bayanta Virgil van Dijk da ta yi ba bisa ka'ida ba.

Van Dijk mai shekara 25, na son ya koma Liverpool da murza-leda idan har ya bar Southampton.

Dan wasan tawagar kwallon kafa ta Netherlands, ya sabunta yarjejeniyarsa a Southampton zuwa shekara shida a bara.

Liverpool ba ta nemi izinin tattaunawa da Van Dijk daga Southampton ba.

Har yanzu Liverpool ba ta ce komai kan batun ba, sai dai Southampton ta jaddada cewar ba za ta sayar da mai tsaron bayan nata ba.

Van Dijk ya koma Soutahmpton a Satumbar 2015 daga Celtic kan kudi fam miliyan 13.

Labarai masu alaka