'Yan Madrid 13 aka gayyata tawagar kasashensu

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ronaldo da Pepe za su buga wa Portugal karawar da za ta yi da Latvia

Kimanin 'yan kwallon Real Madrid 13 aka gayyata a tawagar kasashensu domin zuwa wasan sada zumunta da na gasar cin Kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018.

'Yan kwallon da za su buga wa kasashen nasu tamaula sun hada da Varane da Carvajal da Ramos da Nacho da Isco da Morata da Asensio da Navas da Modric da Kovacic da Cristiano Ronaldo da Pepe da kuma James.

Carvajal da Ramos da Nacho da Isco da Morata da kuma Asensio za su buga wa Spain a wasan sada zumunta da za ta yi da Colombia da wasan shiga gasar cin kofin duniya da Macedonia.

Shi kuwa Varane zai buga wa Faransa wasa biyu da za ta yi; wanda za ta ziyarci Sweden da kuma wanda za ta kece raini da Ingila.

Cristiano Ronaldo da kuma Pepe za su buga wa Portugal a wasan da za ta yi da Latvia, su kuwa Modric da Kovacic za su buga karawar da Croatia za ta ziyarci Iceland.

Keylor Navas zai buga wa Costa Rica wasan shiga gasar cin kofin duniya da za ta kara da Panama da kuma wanda za ta yi da Trinidad da Tobago.

Yayin da James zai fafata a karawar da Colombia za ta ziyarci Spain da wadda za ta je Kamaru.

Labarai masu alaka