Kungiyoyi uku daga Catalonia za su buga La Liga

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Barcelona ce ta lashe Copa del Rey na bana

A karshen mako ne kungiyar kwallon kafa ta Girona ta samu gurbin shiga gasar cin kofin La Liga na Spaniya ta badi.

Hakan na nufin kulob uku ne daga Catalonia da suka hada da Barcelona da Espanyol da kuma Girona za su fafata a gasar ta badi.

Rabon da kungiyoyi uku daga yankin su kara a gasar ta La Liga tun shekara 11 da ta wuce, bayan da Barcelona da Espanyol da Gimnastic suka wakilci yankin.

Wannan kuma shi ne karo na 19 da kungiya uku daga Catalonia ke fafatawa a gasar La Liga, bayan da Barcelona da Espanyol da kuma Europa suka fara yi a kakar 1928/29.