Liverpool na neman Martins maimakon Salah

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Martins ya ci kwallo shida ya taimaka aka zura 14 a raga a wasanni 32 da ya yi

Liverpool na tattaunawa da Sporting Lisborn kan a sayar mata da Gelson Martins, bayan da take fargabar Roma za ta tsuga kudi a kan Mohamed Salah.

Wasu rahotanni daga Portugal sun ce Liverpool ta koma zawarcin Martin, bayan da Roma ta ki amincewa da tayin fam miliyan 28 da ta yi a kan Salah.

Ana rade-radin cewar Roma na son ta sayar da Salah dan kwallon tawagar Masar kan kudi fam miliyan 40.

Liverpool ta koma zawarcin Martins dan kwallon Sporting duk da cewa a yarjejeniyar da ya kulla da kungiyar idan zai bar ta sai an biya fam miliyan 50.

Labarai masu alaka