Super Eagles ta shiryawa karawa da Afirka ta Kudu

Hakkin mallakar hoto The NFF
Image caption A karshen mako ne Nigeria za ta fafata da Afirka ta Kudu a wasan shiga gasar cin

Tawagar kwallon kafa ta Nigeria ta kara daura damarar karawa da za ta yi da Afirka ta Kudu a wasan shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a Kamaru a 2019.

Super Eagles za ta karbi bakuncin Bafana-Bafana a ranar Lahadi a filin wasa na Godswill Akpabio da ke Uyo, Akwa Ibom.

Tuni 'yan wasa 24 da aka gayyata suka isa sansanin horo, yayin da Elderson Echiejile da Ahmed Musa da Kenneth Omeruo sune na karshe da suka isa wurin a ranar Talata.

Ogenyi Onazi ne zai jagoranci tawagar Super Eagles din, bayan da ba a bai wa kyaftin John Mikel Obi goron gayyata ba.

Labarai masu alaka