Modric zai bayar da shaida kan zargin cin hanci

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Modric ya koma Madrid daga Tottenham

Ana sa ran dan kwallon Real Madrid, Luka Modric, da na Liverpool Dejan Lovren za su bayar da shaida kan zargin cin hanci a Croatia.

Masu shigar da kara a Croatia ne za su gurfanar da tsoffin jami'an Dinamo Zagreb, amma ba a zargin 'yan wasan da aikata ba daidai ba.

Modric zai bayar da shaida kan cinikinsa da aka yi daga Dinamo zuwa Tottenham a shekarar 2008.

Shi kuwa Lovren zai bayyana abin da ya sani kan komawa Lyon da ya yi da murza-leda daga Dinamo a shekarar 2010.

Daga baya ne Modric ya koma Real Madrid da taka-leda, shi kuwa Lovren ya je Southampton daga nan kuma ya koma Liverpool.

A watan Afrilu aka fara sauraren zargin cin hanci da ake yi wa tsohon babban jami'in Dinamo Zdravko Mamic da wasu mutane uku.

Shi ma koci Zoran Mamic da tsohon daraktan kungiyar Damir Vrbanovic da wani jami'in karbar haraji.

Dukkan wadanda ake zargi sun ce ba su da laifi.

Labarai masu alaka