Chelsea ba ta bukatata — Costa

Diego Costa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Costa ya ci wa Chelsea kwallo 20 a kakar wasa ta bana

Dan wasan Chelsea Diego Costa ya ce manajan kungiyar Antonio Conte ya shaida masa cewa ba ya bukatarsa a yanzu.

Dan wasan mai shekara 28, ya ci kwallo 20 a wasan 35, da ya buga wa Chelsea a bana.

Costa ya ce:"Ni dan wasan Chelsea ne, amma ba sa so na a kungiyar.

"Antonio Conte ya tura min sako cewa ba zai ci gaba da sanya ni wasa ba a kungiyar, wanna shi ne lamarin. Conte ya ce ba zai sanya ni cikin wadanda zai yi amfani da su a kaka mai zuwa ba".

Costa dan kasar Brazil, wanda ke takawa tawagar Spaniya wasa ya koma Chelsea ne daga Atlentico madrid kan kudi fam miliyan 32 a shekarar 2014.

Costa ya yi shekara hudu a Atlentico, watakila ya koma can da taka-leda, duk da cewa an haramta wa kungiyar daukar 'yan wasa har zuwa watan Janairu.