Man City ta kammala daukar Ederson Moraes

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A watan Maris din bara ne, Moraes dan kwallon tawagar Brazil ya fara buga wa Bencica

Manchester City ta kammala cinikin mai tsaron ragar Benfica, Ederson Moraes, kan kudi fam miliyan 35.

Dan wasan mai shekara 23, ya fara yi wa Benfica kwallo a watan Maris din bara, inda ya lashe kofin Portugal da na kalubalen kasar.

Ederson wanda zai koma Ettihad ta taka-leda a farkon watan Yuli ya ce 'Yana matukar kaunar Manchester City da yadda take gudanar da wasanninta'.

Mai tsaron ragar ya ce 'Ya yanke hukuncin komawa can ne, bayan da Pep Guardiola ke kokarin hada matasan 'yan wasa da kungiyar za ta mora a gaba'.