U-20: Ingila ta kai wasan karshe a karon farko

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wannan ne karon farko da tawagar matasa ta maza 'yan kasa da shekara 20 ta Ingila ta kai wasan karshe a gasar kofin duniya

A karon farko tawagar kwallon kafa ta maza ta matasa 'yan kasa da shekara 20 ta Ingila ta kai wasan karshe a gasar cin kofin duniya bayan da ta doke Italiya 3-1.

Ingila wadda Paul Simpson ke jagoranta ce ta mamaye wasan bayan da aka dawo daga hutu, kuma dan wasan Liverpool, Dominic Solanke ne ya ci kwallo biyu.

An kusa tashi daga karawar dan wasan Everton, Ademola Lookman ya kara ta uku a bugun kwallon da ya yi daga yadi na shida.

Italiya ce ta fara cin kwallo a minti na biyu da fara tamaula ta hannun dan wasan Juventus, Riccardo Orsolini.

Ingila za ta kara a wasan karshe da Venezuela wadda ta fitar da Uruguay a wasan daf da karshe a gasar.

Labarai masu alaka