A Barcelona zan yi ritaya - Messi

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Lionel Messi ya ci wa Barcelona kwallo sama da 500

Dan kwallon tawagar Argentina, Lionel Messi ya ce zai so ya yi ritaya daga murza-leda a Barcelona.

Messi mai shekara 29, ya koma Barcelona yana da shekara 13, ya kuma fara buga mata tamaula yana da shekara 17, ya zuwa yanzu ya ci mata kwallo sama da 500.

Dan wasan ya ce 'abin da yake mafarki yake kuma son gani a kodayaushe ya kammala wasanninsa a Barcelona.

Messi ya lashe kofin La Liga takwas a Barcelona da na Zakarun Turai hudu da kyautar Ballon d'Or ta dan kwallon da ya fi yin fice a duniya sau biyar.

Labarai masu alaka