Real Madrid za ta zabi sabon shugaba

Hakkin mallakar hoto Real Madrid
Image caption Florentino Perez ne ke jan ragamar kungiyar a karo na biyu tun daga shekarar 2009

Kwamitin zabe na kungiyar Real Madrid ya amince a gudanar da zaben shugaba da daraktoci da za su ja ragamar kungiyar.

Tuni kwamitin ya tsayar da ranar 9 zuwa 18 ga watan Yuni domin tantance 'yan takara da wadanda suka dace a zaba.

A kwana daya tsakani za a sanar da wadanda suka cika ka'idar da ake bukata ta jan ragamar Real Madrid wadda ta ci kofin Zakarun Turai guda 12 a tarihi.

Florentino Perez ne ke jan ragamar kungiyar a karo na biyu tun daga shekarar 2009, ya fara shugabantar Madrid a shekarar 2000 zuwa 2006.

Perez ya karbi jan ragamar Real Madrid a hannun Ramon Mendoza.