Usain Bolt ya lashe tseren mita 100 a Jamaica

Usain Bolt Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Bolt ya fara tseren ne kamar ba zai kai labari ba, amma daga bisani kuma sai ya samu nasara

Usain Bolt ya lashe tseren gudun mita 100 na ƙarshe a ƙasarsa ta haihuwa wato Jamaica, gabanin ya yi ritaya daga wasa a watan Agusta mai zuwa a gasar Landan.

A ƙarshen gasar da Bolt ya samu nasara, dan wasan ya yi bankwana da magoya bayansa kimanin dubu 30 a Kingston, babban birnin Jamaica.

Ɗan wasan mai shekara 30 da haihuwa zai yi ritaya ne a watan Agusta mai zuwa bayan Wasan Zakarun Duniya da za a yi a birnin Landan.

Bolt wanda sau takwas yana lashe lambar zinare a Gasar Olympics, ya kammala gudun ne a daƙiƙa 10.03, wanda hakan ya sa 'yan kallon barkewa da shewa da rawa yayin da suke ɗaga tutar kasar.

Bolt wanda shi ne zakaran tseren mita 100 da kuma 200 na duniya, ya sumbace filin tseren gabanin ya yi wata irin tsayuwa da ya saba yi.

Labarai masu alaka