Tsohon ɗan wasan Arsenal Gnabry ya koma Bayern

Dan wasa Serge Gnabry Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gnabry ya zura ƙwallaye 11 a wasanni 27 da ya buga a Gasar Bundesliga

Kulob ɗin ƙwallon ƙafa na Bayern Munich ya saye tsohon ɗan wasan gaban Arsenal, Serge Gnabry, bisa kwantiragin shekara uku.

Ɗan wasan Jamus ɗin, mai shekara 21, ya koma Arsenal ne a shekarar 2012.

Daga nan ne sai West Brom ta karɓi aron shi, kafin daga bisani ya koma kulob ɗin Werder Bremen a kakar bara.

Ya yi wasa mai kyau a kakar bara, inda ya zura ƙwallaye 11 a wasanni 27 da ya buga a Gasar Bundesliga.

Ya ce: "Babban abin alfahari ne na kasance tare da Bayern Munich."

Ya ci gaba da cewa: "Wannan wani lokaci ne wanda na daɗe ina jiransa."

Shugaban kulob ɗin Bayern Munich, Karl-Heinz Rummenigge , ya ce "Muna farin ciki mu ga wani matashin ɗan wasa daga tawagar Jamus a kulob ɗin nan. Gnabry ya samu gogewa sosai a Werder Bremen."

Labarai masu alaka