Man Utd ta sayi Victor Lindelof daga Benfica a kan fam 31

Victor Lindelof Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Victor Lindelof ya koma kulob ɗin Benfica a shekarar 2012

Kulob ɗin Manchester United ya saye ɗan wasan Benfica, Victor Lindelof, a kan fam miliyan 31.

Man U ya ce yarjejeniyar sayen ɗan wasan yanzu tana jiran wasu matakan amincewa da za a yi a mako mai zuwa.

Lindelof, wanda ya buga wa ƙasarsa wato Sweden wasa har sau 12, har ila yau, ranar Talata zai buga mata wani wasan sada zumunta da za su yi da ƙasar Norway.

Ɗan wasan mai shekara 22 wanda ya koma kulob ɗin Benfica a shekarar 2012, shi ne zai zama ɗan wasa na farko da Man U ta saya a kakar bana.

Lindelof ya yi wa Benfica wasa sau 47 a kakar bara, inda ya taka muhimmiyar rawa lokacin da kulob ɗin ya lashe kofin lig ɗin kasar.

Labarai masu alaka