Nadal ya lashe kofin French Open

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Nadal ya lashe French Open na 10 a tarihi

Rafael Nadal ya kafa tarihin lashe kofin Frensh Open karo na 10, bayan da ya doke Stan Wawrinka a Paris a ranar Lahadi.

Nadal mai shekara 31, ya yi nasara da ci 6-2 6-3 6-1, wanda hakan ya bashi damar cin babbar gasar tennis ta 15.

Da wannan nasarar ya sa ya zama mutun na farko da ya lashe babar gasar tennis 10 a tarihin wasan.

Wannan ne karon farko da aka doke Wawrinka a wasan karshe bayan da ya ci uku a baya.