Capello ya koma horar da Jiangsu Suning

Fabio Capello Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Capello ya horar da tawagar kwallon kafa ta Ingila

Kungiyar kwallon kafa ta Jiangsu Suning ta China ta nada Fabio Capello a matsayin kociyanta.

Capello mai shekara 70, ya bi sahun Luis Felipe Scolari da Andre Villas-Boas da Gus Poyet da kuma Felix Magath a matsayin masu horar da tamaula a China.

Tsohon kocin Chelsea, Scolari ne ke jan ragamar kungiyar da ta lashe kofin gasar China, wato Guangzhou Evergrande.

Shi kuwa takawaran Capello, Marcello Lippi shi ne ke horar da tawagar kwallon kafa ta China.

Capello ya yi suna a AC Milan a tsakanin 1990, inda ya ci kofin Seria A hudu da na zakarun Turai.

Ya kuma lashe La Liga sau biyu a Spaniya tare da Real Madrid daga baya ya ci kofin gasar Italiya da Roma.