Vallejo zai maye gurbin Pepe a Madrid

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Vallajo yana yi wa tawagar kwallon kafa ta matasa 'yan kasa da shekara 20 ta Spaniya wasa

Real Madrid ta tabbatar cewar Jesus Vallejo ne ya kamata ya maye gurbin Pepe a kakar wasan 2017 in ji jaridar Marca.

Vallejo mai shekara 20, dan kwallon Real Madrid wanda ke taka-leda aro a Eintracht Frankfurt ya yi fama da jinya a raunin da ya ji a watan Fabrairu a gasar Bundesliga.

Jaridar ta ce tuni Madrid ta fara tuntubar dan kwallon domin jin ra'ayinsa da shirye-shiryen da zai yi don komawa Spaniya da taka-leda.

Ana sa ran mai tsaron bayan zai fara atisaye da Real Madrid a farkon kakar bana da zarar an kammala gasar nahiyar Turai ta matasa 'yan kasa da shekara 20 da Spaniya ke bugawa.

Labarai masu alaka