Tijjani zai jagoranci NBBF karo na uku

Basket Ball
Image caption Wannan ne karo na uku da Tijjani zai ja ragamar hukumar kwallon kwando ta Nigeria

An zabi Tijjani Umar a matsayin shugaban hukumar kwallon kwando ta Nigeria a karo na uku.

A zaben da aka gudanar a jihar Kano ta Nigeria a ranar Litinin, Tijjani zai ci gaba da jan ragamar hukumar zuwa 2021.

Bayan da aka rantsar da shugaban ya ce 'Zai mayar da hankali wajen zakulo yara matasa da za su wakilci kasar a nan gaba da samar da kudaden da za a dinga gabatar da wasanni a kasar'.

Sauran wadanda aka zaba sun hada da Olumide Oyedeji da Alhaji Muktar Kaleh da Dakta Joseph Adeyemo da Mustapha Sulaiman.

Haka ma Segun Famuyiwa da Ejike Paul da Stanley Gumut da Uwargida Margaret Porbeni suna daga cikin wadanda za su ja ragamar hukumar zuwa shekara hudu.

Labarai masu alaka