Iran ta kai gasar kofin duniya a karon farko

World Cup 2018 Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Tsohon mataimakin kocin Manchester United, Carlos Queiroz ne ke horar da Iran

Kasar Iran ta zama ta biyu da ta samu tikitin shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018, bayan da ta doke Uzbekistan 2-0 a Tehran.

Iran wadda Carlos Queiroz ke jagoranta ta ci kwallo ta hannun Sardar Azmoun da kuma Mehdi Taremi.

Brazil wadda ta lashe kofin duniya karo biyar, ita ce ta farko da ta fara samun gurbin shiga gasar da za a yi a Rasha.

Kungiyoyin da suka yi na daya da na biyu ne ke zuwa gasar kofin duniya a rukunin nahiyar Asia, yayin da kasar da ta yi ta uku ke buga wasannin cike gurbi.

Labarai masu alaka