Ana zargin Ronaldo da ƙin biyan haraji

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ronaldo ya ci kofin Zakarun Turai a lokacin da Real Madrid ta ci Juventus 4-1

Masu shigar da kara a Spaniya sun zargi dan kwallon Real Madrid, Cristiano Ronaldo da yin zambar kudin haraji na miliyoyin Yuro.

Ofishin masu shigar da karar a Madrid ya ce ya shigar da karar dan kwallon tawagar Portugal da kin biyan harajin Yuro miliyan 14.7 daga tsakanin 2011 zuwa 2014.

Ronaldo wanda shi ne dan wasan da ya fi karbar albashi a duniya a tsakanin masu wasanni ya fada a baya cewar bai damu da binciken da ake yi masa kan haraji ba, domin babu abin da zai boye.

A watan Disemba, wasu bayanan da aka kwarmanta sun nuna cewa Cristiano Ronaldo, ya kauce biyan haraji kan kudadan dake asusunsa a kasashen waje.

Dan kwallon ya karyata zargin da ake yi masa.

Labarai masu alaka