Everton ta dauki mai tsaron raga Pickford

Sunderland Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Pickford ya taka rawar gani a Sunderland a kakar da aka kammala

Kungiyar Everton ta cimma yarjejeniyar daukar mai tsaron ragar Sunderland, Jordan Pickford kan kudi fam miliyan 30.

Idan Pickford mai shekara 23 ya saka hannu kan yarjejeniyar, ya zama gola dan Burtaniya da ya fi tsada a tarihi.

Mai tsaron ragar ya buga wa Sunderland wasa 29 a bana, duk da hakan bai hana kungiyar faduwa daga gasar Premier da aka kammala ba.

Pickford ya koma kungiyar matasa ta Sunderland a 2010, bayan da ya yi wasa aro a Darlington da Alfreton Town da Burton Albion da Carlisle United da Bradford City da kuma Preston.