Nantes ta dauki Claudio Ranieri

Leicester City Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ranieri ya lashe kofin Premier a 2015-16 a Leicester City, amma ta raba gari da shi a bana

Kungiyar Nantes ta nada tsohon kocin Leicester City, Claudio Ranieri a matsayin wanda zai horar da ita tamaula.

Ranieri ya karbi aikin ne, bayan da hukumar kwallon kafar Faransa ta amince ya ja ragamar kungiyar duk da cewar yana da shekara 65 wadanda suka wuce ka'idar horar da tamaula a kasar.

Kocin dan kasar Italiya ya jagoranci Leicester City ta lashe kofin Premier a karon farko a 2015-16.

A watan Fabrairu Leicester ta raba gari da kociyan bayan da kungiyar ta kasa takarawar gani a gasar Premier da aka kammala.

Nantes ta amince da kocinta Sergio Conceicao ya koma Portugal domin jan ragamar FC Porto.