Ronaldo ya musanta zargin kin biyan haraji

Cristiano Ronaldo Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ronaldo dan kwallon Real Madrid da tawagar Portugal

Masu shigar da kara a Spaniya sun zargi dan kwallon Real Madrid, Cristiano Ronaldo da yin zambar kudin haraji na miliyoyin Yuro.

Ofishin masu shigar da karar a Madrid ya ce ya shigar da karar dan kwallon tawagar Portugal da kin biyan harajin Yuro miliyan 14.7 daga tsakanin 2011 zuwa 2014.

A wani jawabi da masu wakiltar dan kwallon suka fitar ya ce 'babu wani yunkurin boye bayanan kudi da Ronaldo ya yi domin kaucewa biyan haraji'.

Ronaldo wanda shi ne dan wasan da ya fi karbar albashi a duniya a tsakanin masu wasanni ya fada a baya cewar bai damu da binciken da ake yi masa kan haraji ba, domin babu abin da zai boye.

A watan Disemba, wasu bayanan da aka kwarmanta sun nuna cewa Cristiano Ronaldo, ya kauce biyan haraji kan kudadan dake asusunsa a kasashen waje.

Dan kwallon ya karyata zargin da ake yi masa.

Labarai masu alaka