Real Madrid: Ronaldo baya wasa da biyan hakki

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ronaldo ya koma Madrid a 2009 daga kungiyar Manchester United

Kungiyar Real Madrid ta fitar da wata sanarwar cewa tana da yakinin Cristiano Ronaldo na bin ka'ida wajen sauke hakkin doka da ke kansa.

Madrid ta ce tun lokacin da Ronaldo ya koma kungiyar a Yulin 2009, ya nuna aniyarsa karara kan yadda yake biyan dukkan harajin da suke kansa.

Haka kuma kungiyar ta ce Cristiano Ronaldo zai wanke kansa kan zargin kin biyan haraji da ake yi masa.

Masu shigar da kara a Spaniya ne ke zargin dan kwallon Real Madrid, Cristiano Ronaldo da yin zambar kudin haraji na miliyoyin Yuro.

Ofishin masu shigar da karar a Madrid ya ce ya shigar da karar dan kwallon tawagar Portugal da kin biyan harajin Yuro miliyan 14.7 daga tsakanin 2011 zuwa 2014.

Ronaldo ya karyata aikata ba daidai ba.

Madrid din na fatan gaskiya za ta yi halinta nan ba da jimawa ba.

Labarai masu alaka