Abidal ya zama jakadan Barcelona

Barcelona Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Abidal ya bar Barcelona a shekarar 2013

Kungiyar Barcelona ta nada tsohon dan wasanta Erik Abidal a matsayin jakada a ranar Laraba.

Barcelona ta ce ta cimma yarjejeniya da Abidal mai shekara 37, domin ya zama jakadanta a dukkan wasu abubuwa da za ta gudanar da suka hada da wakiltar tsoffin 'yan wasanta.

Tsohon dan wasan zai kuma wakilci kungiyar a bukukuwan da makarantu ke shiryawa da na sada zumunta tsakanin magoya baya da suka shafi Barcelona.

Abidal ya yi shekara shida a Barcelona, inda ya buga mata wasa 193, ya kuma lashe kofi 15 daga ciki har da na La Liga hudu da na Zakarun Turai biyu.

Dan kwallon ya bar Camp Nou a shekarar 2013.