Man United ta kammala cinikin Lindelof

Manchester United Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption Victor Lindel ya koma Benfica da murza-leda daga kungiyar Vasteras SK

Manchester United ta kammala sayen dan kwallon Benfica, Victor Lindelof kan kudi fan miliyan 31.

A ranar Laraba dan kwallon tawagar Sweeden ya je Manchester United, inda aka duba lafiyarsa sannan ya saka hannu kan yarjejeniya.

Dan kwallon mai shekara 22, ya zama mai tsaron baya da United ta saya mafi tsada a tarihi.

United ta dauki Rio Fredinand a shekarar 2002 kan kudi fam miliyan 29.1 a matakin wanda ya fi tsada a lokacin.

Manchester United za ta karbi bakuncin West Ham United a gasar cin kofin Premier ta 2017/18.

Labarai masu alaka