Watakila 'yan wasa shida su bar Madrid

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Real Madrid ce ta dauki La Liga da Kofin Zakarun Turai

Real Madrid ta yi fice wajen sayen 'yan wasan kwallon kafa mafiya tsada a duniya, sai dai wannan karon ita ce za ta karbi makudan kudin da ake zawarcin 'yan wasanta.

Watakila 'yan kwallon Real Madrid shida ne ake sa ran za su sauya sheka da zarar an bude kasuwar saye da sayar da 'yan wasan kwallon kafa ta bana.

Cikin 'yan kwallon da ake hasashen za su bar Santiago Bernabeu sun hada da Fabio Coentraro da Pepe da James Rodriguez da Alvaro Morata da Diego Llorente da kuma Mariano Diaz.

Shi Coentraro ana rade-radin Sporting Lisborn zai koma taka-leda aro, Pepe kuwa yarjejeniyarsa ce za ta kare a karshen watan Yuni, kuma kila Paris zai koma buga tamaula.

Sauran 'yan wasa hudun da suka rage a nan ne Real Madrid za ta karbi kudin da ake cewa zai kai Yuro miliyan 160.

Madrid ba ta son sayar da Morata wanda Manchester United ke zawarci kan kudi kasa da Yuro miliyon 90, haka kuma kungiyar na sa ran samun Yuro miliyan 70 kudin James Rodriquez.

Real Sociedad na zawarcin Llorente kan Yuro miliyan 8, shi kuwa Mariano Diaz zai iya barin Barnabeu kan Yuro miliyan 5.

Labarai masu alaka