Bayern za ta kara da Liverpool a Audi Cup

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Bayern ce ta lashe kofin Bundesliga da aka kammala

Bayern Munich ta ce za ta fafata da Liverpool a wasan share fage a gasar Audi Cup, domin tunkarar kakar tamaula mai zuwa a ranar 1 ga watan Agusta.

A sanarwar da kungiyar ta fitar a ranar Alhamis ta ce daya wasan za a yi shi ne tsakanin Atletico Madrid da Napoli.

A ranar 2 ga watan Agusta ake sa ran buga wasan karshe, bayan kungiyoyin sun fafata a jadawalin da aka fitar.

Bayern wadda ta ci Bundesliga na biyar a jere a bana za ta fara wasannin tunkarar kakar badi a ranar 1 ga watan Yuni daga nan ta ziyarci Asia sannan ta dawo Jamus ta buga Audi Cup.

Napoli da Atletico Madrid wadan da suka yi na uku a gasar kasashensu za su buga gasar cin kofin Zakarun Turai, Liverpool kuwa wadda ta yi ta hudu a gasar Premier za ta fafata a wasannin cike gurbin wasan.