An kori koci bayan da aka doke kungiyarsa 25-0

Spanish Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Cin da aka dinga yi wa kungiyar ya girgiza jami'anta

An sallami kocin wata kungiyar matasan kwallon kafa a Spaniya, bayan da aka doke su 25-0.

Kungiyar ta matasan Serrano ta raba gari da kocin inda ta ce kwallayen da aka zura musu a raga sun wuce tunani.

Rahotanni daga jaridun Spaniya sun ce Lauyan kocin ya ce 'mai horarwar bai matsa wa matasan sai sun ci kwallo ba a karawar'.

'Kocin ya umarci matasan su saka matsi zuwa tsakiyar filin wasa, inda suka dinga kai hari amma suka bar baya da baraka' in ji Lauyan.

Karawar da suka yi ita ce ta karshe a kakar bana, inda suka kammala a mataki na karshe ba tare da maki ba, bayan da aka zura musu kwallo 247 a wasa 30 da suka yi.

Labarai masu alaka