Damben Boksin: Mayweather ya zaku ya kara da Conor McGregor

Floyd Mayweather da Conor McGregor. Hakkin mallakar hoto others
Image caption Mayweather mai shekara 40 zai kara da Conor McGregor mai shekara 28

Tsohon zakaran damben boksin Floyd Mayweather ya ce zai ba wa mutane abin da suke sha'awar gani yayin da zai dawo daga murabus din da ya yi daga wasan domin gwabzawa da zakaran damben hannu da kafa Conor McGregor.

Tsohon zakaran ajin matsakaita nauyin na duniya, Mayweather mai shekara 40, ya yi ritaya ne a 2015, bayan dambe 49 da ya yi ba tare da an doke shi ba.

Ba'amurken zai kara ne da McGregor dan Ireland, mai shekara 28, a Las Vegas ranar 26 ga watan Agusta.

Ana ganin kowanne cikin 'yan damben matsakaita nauyi biyu zai samu ladan da ya kai na dala miliyan 100 idan suka fafata.

Tun bayan da Mayweather ya doke Andre Berto a watan Satumba na 2015 bai sake wani dambe ba, kuma wannan na yanzu zai iya kara masa bajinta ta dambe 50 ba tare da an doke shi ba.

Idan kuma ya gamu da bacin rana, aka doke shi , hakan zai zama wani tabo a rayuwarsa ta damben boksin, wanda aka kai shi kasa a karawa 50 kenan.