Damben Boksin: Malamin makaranta zai kara da Manny Pacquiao

Manny Pacquiao da Jeff Horn Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Pacquiao ya yi rashin nasara a uku daga cikin dambensa takwas na karshe

Wani malamin koyar da darasin motsa jiki a kasar Australia wanda kusan ba a san shi ba na shirin yin dambe da zakaran matsakaita nauyi na duniya Manny Pacquiao.

Idan malamin, Jeff Horn mai shekara 29 ya yi nasara a damben na ranar biyu ga watan Yuli to ba shakka rayuwarsa za ta iya sauyawa har abada.

Shi dai Horn shekara 11 da ta wuce ne ya je ya shiga wata kungiya ta wasan damben boksin domin ya koyi wasan domin kare kansa.

A lokacin da yake dalibi a makaranta ya karanta littattafai, da wasannin dara kuma ya rika shiga halin ni-'yasu a hannun manyan dalibai, saboda cin zalinsa da suke yi.

A kan haka ne ya fara sha'awar boksin har ya rika shiga gasa a lokacin yana dalibin, ko da yake kamar yadda ya sheda wa BBC bai yi nasara a yawancin gasar da yake shiga ba a lokacin.

A shekara ta 2012 Horn ya kai wasan dab da na kusa da karshe a gasar Olympic, lokacin yana karatunsa na digiri, kuma daga nan ne ya shiga wasan gadan-gadan a matsayin kwararre.

Yanzu cikakken aikinsa shi ne damben boksin kuma shi ne na biyu a duniya a rukunin matsakaita nauyi bayan Pacquiao.

Abokin karawar tasa Manny Pacquiao mai shekara 38, wanda ke rike da kambin duniya na matsakaita nauyi, dan majalisar dattawa ne a kasarsa Philippines.